Ba Laifin Tinubu Bane Don Majalisa Ta Ki Sahhalewa El-Rufai Ya Zama Minista, Bagudu
- Minsitan kasafin kudi da tsara tattalin arziki ya tabo batun da ya shafi kin amincewa da El-Rufai cikin ministocin Tinubu
- A cewarsa hakkin majalisa ne amincewar, don haka ba za a ga laifin Tinubu wajen kin amincewar majalisar
- Kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba majalisar dattawa damar tantancewa tare da duba nagartar ministoci kafin amincewa dasu
FCT, Abuja - Ministan kasafin kudi da tsara tattalin arzikin Najeriya, Atiku Bagudu ya ce, ba laifin Shugaba Bola Ahmad Tinubu bane don majalisar kasa ta ki sahhalewa Nasir El-Rufai ya zama minista a gwamnatin nan.
A cewar Bagudu, Tinubu ya cika alkawari wajen mika sunan El-Rufai a jerin ministocinsa da ya nemi majalisar ta tantance don yin aiki tare dashi.
Ya bayyana cewa, majalisar ce ta ga dacewar kin amincewa da El-Rufai tare da tabbatar dashi a matsayin ministan, rahoton Premium Times.
Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa
Ba laifin Tinubu bane rashin amincewa da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tattaunawa da jaridar, ya ce tsarin demokradiyya da kundin tsarin kasar ne ya ba majalisar ikon tantancewa da amincewa da nagartar ministoci.
Ya kara da cewa:
"Shugaban kasa bai da wani katabus a kudin tsarin mulkin kasa ya yi wani abu. Hakan daidai ne? Amma haka aka tsara dokar."Yadda El-Rufai ya yi kokari a kamfen Tinubu
A lokacin gangamin neman zaben Tinubu, El-Rufai na daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen tattabar da nasarar jam'iyyar APC a zaben 2023.
Kafin zaben, Tinubu ya bayyana rokonsa ga El-Rufai a idon duniya, inda yace yana sha'awar aiki dashi idan ya zama shugaban kasa.
A watan Agustan bara ne aka mika sunan El-Rufai cikin jerin ministoci, amma majalisa ta ki amincewa da shi a matsayin wadanda za su yi aiki da Tinubu.
Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari
Babu wata matsala tsakanin El-Rufai da Tinubu
A bangare guda, jigon jam'iyyar APC a jihar Plateau, Podar Yiljwan Johnson ya magantu kan alakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Nasir El-Rufai.
Johnson ya ce babu wata matsala tsakanin Tinubu da Nasir El-Rufai kamar yadda ake zargi a wasu bangarori.
Sai dai, har yanzu Shugaba Tinubu ko El-Rufai babu wanda ya bayyana alakar da ake da ita a tsakanin juna.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn56gZRmmZplnJa2p7XNZquipqWXwm6uwKecZpyfo3qurcmao6KrkWLBonnKomSsmZidrq2x1ppknqRdp8KnrchmsJplqpa6onnMoqWiq6SWeqOtxq6brmc%3D